KAI TSAYE: Yadda zaben fidda gwani na APC ke gudana a jihohin kasar nan

0

Jihar Zamfara: Darektan yada labarai na jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, Shehu Isa ya bayyana cewa an dage zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka yi shirin gudanarwa yau Lahadi a jihar.

Shehu ya ce hakan ya biyo bayan rashin isowar shugabannin hukuma Zabe ne da za su kula da yadda za a gudanar da zaben.

An dage zaben zuwa ranar 1 ga watan Oktoba.

Jihar Kaduna: Dubban deliget sun halarci filin wasa na Murtala Square dake cikin garin Kaduna domin zaben dan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar APC, gwamna mai ci Nasir EL-Rufai.

Shine dan takara daya tilo da yake takarar.

Jihar Bauchi: An koka game da rshin isowar kayan zabe da wuri.

Jihar Ogun: An dage Zaben fidda gwani na gwamnan jihar.

Jihar Kano: Deliget sun zabi gwamnan jihar Abdullahi Ganduje a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Jihar Legas: An dage zaben fidda gwani na jihar Legas. Za ayi zaben ranar Litinin.

Jihar Jigawa: Ana tantance wakilan da za suyi zabe a wani gidan hutawa dake mallakar gwamnatin jihar ne. Da zarar an kammala wannan tantancewa za a dauke cak gaba dayan su zuwa filin da za a kada kuri’a.

Ubale Hashim ne da gwamna Mohammed Badaru za su gwabza.

Share.

game da Author