Gwamnatin Ribas ta nemi Amaechi ya amayo naira Biliyan 112 na kadarorin da ya sayar

0

Gwamnatin Jihar Rivers ta bayyana cewa Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya na da tuhuma a kan sa dangane da zargin karkatar da kudaden tashar makamashin gas da ya sayar.

Tashar wadda a lokacin da Ameachi ke gwamnan jihar Ribas, ya sayar da ita ne ga kamfani mai zaman kan sa.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Emma Okah, ya bayyana haka a ranar Litinin, ya na mai kara bayanin cewa Amaechi ya saida tashar samar da gas din ce ga kamfanin mai na Sahara Energy, mallakar wani hamshakin attajiri mai suna Tonye Cole.

An saida tashar ce a daidai lokacin da wa’adin Amaechi ke kusa da karewa a shekarar kafin zaben 2015.

Okah ya ce yayin da Amaechi ya sayar da tashar gas din har naira bilyan 112, ya yi amfani da kudin ne wajen gudanar da yakin neman zaben APC, wanda Amaechi din shi ne jagoran ta a jihar Rivers kuma shi ne Babban Daraktan Yakin Neman Zaben Muhammadu Buhari a lokacin.

Kwanan baya ne shi ma Cole ya sauka daga shugabancin kamfanin Sahara Energy da nufin shiga cikin siyasa, ka’in-da-na’in.

Ana yada labarin cewa shi ne Amaechi ke son ya zama dan takarar gwamnan jihar Rivers a karkashin APC a zaben 2019.

“Ai yanzu dai dalilin fitowa takarar Tonye Dele Cole a karkashin APC ya fito fili. Ana so ne a rufe barnar da Amaechi ya tafka, wadda kuma shi Cole din ne ya sayi kamfanin a lokacin daga hannun gwamnatin jihar Ribas, a lokacin da Amaechi ke gwamna.

Okah ya ci gaba da saboda Amaechi ya karkatar da kudin wajen kamfen din APC a lokacin, hakan ya haddasa kasa kammala wasu ayyuka da ya fara, kuma ya kasa biyar ma’aikata albashi da kudaden fanshon su, kafin ya bar ofis.

Kwamishinan ya kara da cewa, Sahara Energy shi ne kuma ya sayi Olympia Hotel da sauran wasu manyan kadarorin jihar masu tsadar gaske.

Ya ce kuma duk an yi cinikin a cikin yanayi na rufa-rufa da rub-da-ciki.

“Bayan ya sauka gwamnatin Nyesom Wike ta hau, an kafa Kwamitin Bincike na Omejire, inda ya samu Amaechi da hannu dumu-dumu na salwantar naira biliyan 112. Maimakon ya maido kudaden, sai ya garzaya kotu, ya nemi kotu ta bayar da sammacin yin watsi da sakamaon binciken.

“Amaechi bai yi nasara a Babbar Kotu ba, kuma bai hakura ba, sai ya sake yin gaba, ya garzaya Babbar Kotun Daukaka Kara. A can ma din bai yi nasara ba.

“Har wa yau Amaechi ya tafi Kotun Koli gaba daya, amma a can an yi watsi da batun, an daina magana a kai, saboda har yau sama da shekara daya kenan Amaechi bai tura wa Kotun Koli ba’asin bayanan da su ka kamata ya bayar wanda ya sani dangane da inda kudaden suke ba.”

Kokarin da PREMIUM TIMES ta yin a jin ta bakin Amaechi ya ci tura. Yayin da Kwamishina Okah ya ce duk wata barazana da Amaechi zai yi wa jihar Ribas, a wannan lokacin ba ta yi wani tasiri ba.

Share.

game da Author