Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar kan a hana tilasta wa majalisa ta dawo zama kafin ranar 25 ga Satumba

0

Babban Kotu dake Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar gabantakan a hana tilasta wa majalisa ta dawo zama kafin ranar 25 ga Satumba.

Wasu sanatoci ne dake tare da shugaban Majalisar Bukola Saraki, Sanata Isah Misau da Sanata Rafiu Adebayo suka shigar da karar.

Sun nemi koto da ta dakatar da kokarin da ake yi na a tilasta wa sanatoci su dawo daga hutun da suke a yanzu.

Alkalin ya bayyana cewa wannan kara da aka shigar ba ta da ma’ana wadda a dalilin haka ya yi watsi da karar.

Share.

game da Author