TSARE DAN JARIDA: Kotu ta umarci gwamnati biyan Abiri diyyar naira miliyan 10

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayyana cewa tsarewar da jami’an SSS suka yi wa dan jarida Jones Abiri har tsawon shekaru biyu, ya nuna kenan an yi kasassabar yanke masa hukunci.

Don hana nan take sai Mai Shari’a Nnamdi Dimgba ya umarci gwamnatin tarayya ta biya shi diyyar naira miliyan 10, ladar tsarewar tsawon shekaru biyu da aka yi masa.

An kama Abiri tun cikin watan Agusta, 2016, kuma aka tsare shi tsawon wannan lokacin har sai da lauyoyi, kungiyoyin kare hakkin dan adam karkashin jagorancin Femi Falana suka shigar da karar Gwamnatin Tarayya a kotu, sannan aka sake shi.

Kafin sakin sa, ganin an matsa lamba, sai aka gurfanar da shi kotu a bisa tuhumar sa da laifin ta’addanci a yankin Neja-Delta.

Da ya ke yanke hukunci a yau Alhamis dangane da Jones Abiri, Dimgba ya ce gwamnatin tarayya ba ta da wani dalili ko hujjar tsare Abiri, tunda daga ranar da ya rubuta bayanin sa a hannun SSS cikin watan Agusta, 2016.

“Tunda an sa ya rubuta bayanai da kan sa, don me kuma za a ci gaba da tsare shi? Ai daga ranar ne ya kamata a gurfanar da shi kotu kawai.”

Mai Shari’a ya ce hujjar da gwamnatin tarayya ta bayar cewa wai ta tsare Jones Abiri har tsawon shekara biyu, saboda barazana ne shi ga tsaron kasa, magana ce kawai ta borin-kunya maras makama.

Mai Shari’a ya ci gaba da cewa abin da ya kamata gwamnati ta yi tunda farko, shi ne kawai ta gurfanar da Abiri a kotu, daga nan sai ta nemi kotu kada ta bayar da belin sa. To ita kotun ce za ta duba yiwuwar ci gaba da tsare shi da kuma inda ya kamata a ci gaba da tsare shi ko kuma bada belin sa.

A karshe dai kotu ta ce tsarewar da aka yi wa Abiri haramtacciya ce, kuma an tauye masa ‘yanci da hakkin sa na dan adam.

Share.

game da Author