A yi kaffa-kaffa da tambayoyin Jarabawa da ake watsawa a soshiyal midiya – WAEC

0

Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare ta Afrika ta Yamma (WAEC), ta gargadi dalibai da su guji tambayoyin jarabawar da ake yadawa a soshiyal midiya, ta na mai cewa na karya ne kuma duk bogi ce domin amincewa da su zai iya dakushe kaifin fahimtar dalibi a lokacin amsa tambayoyin jarabawar WEAC.

Kakakin Wayar da Kai na hukumar Damianus Ojijeoru ne ya bayyana haka a cikin wata takardar da ya raba wa manema labarai a yau Alhamis da safe.

Ya je an jawo hankalin hukumar dangane da wata harkalla da wasu mazambata ke yi a soshiyal midiya, wadda ka iya haifar da matsala ga masu rubuta jarabawar fita sakandare ta 2018.

Ya ce ana ta tura tambayoyin jarabawar WAEC ta WhatsAPP da sauran kafafen bogi na soshiyal midiya wadanda tambayoyin nan duk karya ce aka kirkira, ba gaskiya ba ne.”

Ya ce kada dalibai su sake a ribbace su, har ta kai su ga yin biyu-babu.

Ya bada misali da cewa akwai tambayoyin jarabawar da aka rubuta a kasar Saliyo da kuma Gambiya. Amma abin mamaki sai wasu suka rubuta wasu tambaoyin suka ce wai su ne za a tambaya, kuma suka nuna a nan Najeriya ne aka rubuta su.

Share.

game da Author