Buratai da manyan sojoji 49 sun yi jarabawar koyon Hausa, Yarabanci da Igbo

0

Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai, tare da wasu manyan jami’an sojoji 49 sun yi jarabawar koyon harsunan Hausa, Yarabanci da Igbo.

Wannan dai wani gwaji ne da aka shirya domin a tantance kwarewar sojojin a kan koyon wadannan harsuna guda uku da aka hore su da su tabbatar sun koya.

Kakakin Sojoji, Texas Chukwu, ya bayyana cewa an shirya yin gwajin ne, bayan an shafe watanni takwas ana yi wa manyan sojojin lacca a hedikwatar sojojin a Abuja.

Ya ce abin da jojoji suka yi la’akari da kuma yakini shi ne, koyon wadannan harsuna guda uku zai taimaka musu kwarai wajen gudanar da ayyukan samar da tsaro da suke yi a fadin kasar nan.

“Sannan kuma hakan zai karfafa zumunci tsakanin sojoji da kuma jama’a gabadaya.”

Chukwu ya kara da cewa manyan sojojin da suka shiga cikin jarabawar gwajin sun hada da Manyan Jami’an Sojojin Hedikwata, Kwamandoji, Daraktoci da kuma wasu manyan jami’ai.

Ya kara da cewa Laftanar Janar Buratai ya jinjina wa manyan sojojin dangane da da’ar da suka nuna a tsawon lokacin gwajin da aka yi musu.

Ya ce cikin wata mai zuwa za a fito da sakamakon da kowa ya samu a wurin gwajin, sannan kuma sai su sake shirin wata jarabawar.

Share.

game da Author