Tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa akwai matukar bukatar canja tsarin karatun Alkur’ani da ake yi a tsain almajirci, domin ya zamo kafada da kafada da tsarin karatun addinin musulunci na zamani.
A jiya Laraba ne Ribadu ya yi wannan jawabi a wurin addamar da littattafai uku da PREMIUM TIMES ta shirya, inda tsohon shugaban na EFCC ya ce tsarin karatun ya na da amfani, amma kuma karsashin sa sai kara disashewa ya ke yi.
Littattafan da aka kaddamar duk na Turanci ne, da suka hada da “Sect and Social Disorder” da kuma Creed and Creed and Grievance” wadanda Abdul Raufu Mustapha ya gyara sai kuma “Quranic Schools in Northern Nigeria”, wanda Hannah Hoechner ta rubuta.
Ribadu ya kara da cewa irin tsarin da iyaye ke tura kananan yara da sunan almajiranci akasari a hannun wadanda ba su yi musu kyakkayawar kulawa, ya kan tauye almajiran.
Malam ya ce irin wadannan kananan yara masu almajirci kan samu kan su cikin rikice-rikicen da kan ritsa da su kamar irin na Kaduna, Zangon Kataf da sauran wurare.
“Na yi aiki da ya jibinci irin wadannan rikice-rikicen a matsayi na na mamba na kwamitin bincike, na je Zangon Kataf, na je Tafawa Balewa, na je Kaduna kan binciken rikce-rikicen addini.”Inji Ribadu.
“A lokacin rikicin Kaduna a cikin 2000, mun kai ziyara inda aka rufe gawarwakin wadanda aka kashe a kan titin zuwa Birnin Gwari, sun bude mana kaburbura.
“Na ga sama da gawarwakin yara kanana maza wadanda ba a iya gane su, ba wanda ke da sunan sa a rubuce.
Da ya ke bayani, Bishop na Roman Katolika da ke Sakkwato, Mathew Kukah, ya yi kira ga mabanbantan addinai da su rika rungumar juna, sannan kuma a daina tsankiya da juna, abin da ya ce hakan ba zai iya magance rikice-rikice a cikin al’umma ba.