Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, gwamnan jihar Ekiti, sanata Shehu Sani da dubban ‘yan Najeriya sun yi tir da yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya take ci gaba da tsare wakilin PREMIUM TIMES Samuel Ogundipe.
Bayan haka a yau Alhamis ne kungiyar ‘yan jarida ta kasa da daya daga cikin masu takarar shugaban Kasar Najeriya Sowore Omoleye da wasu kungiyoyin rajin kare hakkin dan Adam, suka yi dunguma zuwa ofishin ‘yan sandan Najeriya, suna neman a saki Samuel Ogundipe.
Kakakin rundunar ‘yan sanda, Moshood Jimoh, ya bayyana wa masu zanga-zanga cewa rundunar na kokarin ganin an warware tsakanin ‘yan sanda da wakilin jaridar, sai dai kuma da yake yanzu haka akwai umarnin kotu a kai babu yadda za a yi sai an kai ga wannan lokaci, Inji Moshood.
Idan ba a manta ta rundunar ‘yan sanda sun sulale da Ogundipe a boye zuwa wani Kotun Majistare dake Kubwa inda aka gurfanar da shi ba tare da an bashi damar ganawa da babban darektan kamfanin sa ba ko kuma lauyan sa.
Kungiyar marubuta ta kasar Pakistan ta rubuta wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasika ta musamman tana kira ga resa da ya gaggauta sa baki a wannan abu da yake faruwa da wakilin jaridar PREMIUM TIMES.