Saraki ya kira taron gaggawa da shugabannin Majalisar kasa

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya kira wani taron gaggawa da zai gudanar tare da Shugabannin Majalisar Dattawa da na Tarayya.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa za a gudanar da taron shugabannin bangarorin biyu gobe Talata da rana.

Majiya ta shaida wa Premium Times cewa za a tattauna batutuwan da suka shafi kasa, wadanda ke da bukatar aiwatarwar gaggawa.

Ana sa ran za su yi tattaunawar awa daya da rana.

Sannan kuma da misalin karfe daya daidai na rana, za su gana da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa. Farfesa Mahmood Yaukubu.

Wasu daga cikin batutuwan da ake zaton za su dubba, sun hada da batun goguwar canja sheka da ta dabaibaye jam’iyyu, musamman APC. Sai kuma ji-ta-ji-tar zargin tuggun da aka ce wasu na kokakirn kitsawa domin tsige Saraki.

Dama kuma irin su Sanata Ali Ndume sun yi korafin cewa hutun watanni biyu da Majalisar Dattawa ta dauka ya yi tsawo sosai.

Share.

game da Author