KADUNA-ABUJA: Fasinjojin jirgin kasa sun yi zanga-zangar fushin cuwa-cuwar tikiti

0

Daruruwan fasinjojin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja, sun tada kayar bayan fusata da yadda ake harkalla wajen saida tikitin jirgi daga Kaduna zuwa Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa duk da jirgin da zai dauki fasinja daga Kaduna zuwa Abuja ya isa tashar da ke Rigasa da wuri, sai daruruwan fasinjoji suka yi wa jirgin shinge, suka hana shi isa hanyar da zai karasa ya tsaya ya dauki fasinjoji.

Masu zanga-zangar sun ce minti 10 kacal aka yi ana saida tikiti, sai kawai aka ce wai har tikitin ya kare.

Wani fasinja mai suna Usman Lamin, ya yi zargin cewa jami’an kula da tashar jirgin kasan sun saida sama da tikiti 600 ga ‘yan cuwa-cuwa, wadanda ke rubanya farashin tikitin ga duk wanda zai iya saye.

Mafusatan sun ce tilas sai manajan ya kyale kowa ya shiga jirgin, idan an yi layi, kowa sai ya rika biyan kudin sa bakin kofar shiga jirgi kawai, hakan ne mafita.

Kokarin jin ta bakin jami’an kula da tashar jirgin ya ci tura, amma dai wani ma’aikaci yace mafita a nan kawai ita ce a kara yawan jiragen da ke jigila fiye da guda biyu din da ke yi a kowace ranar Lahadi.

Ya ce saboda tsoron matsalar rashin tsaro a kan titi, ya sa jama’a sun koma hawan jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja.

Har sai da ta kai an yi amfani da sojoji kafin fasinjoji su samu shiga cikin jirgin.

Share.

game da Author