An kafa kwamiti domin wayar wa mutane kai game da ciwon siga a Najeriya

0

Cutar ‘Diabetes’ da a ke kira ciwon siga cuta ce da ake kamuwa da ita sanadiyyar yawan shan zaki ko kuma yawan cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Carbohydrates’.

Bayanai sun nuna cewa ciwon Siga ta kasu kashi daban-daban amma an fi kamuwa da wadda ake kira ‘Type -2 diabetes’.

Sannan kuma rashin motsa jiki da makamantan su na daga cikin abubuwa da ke sa a kamu da wannan cuta. Ita wannan cuta kawai idan har aka kamu da ita za a iya kamuwa da cututta kamar su
cutar koda, shanyewar bangaren jiki hawan jini, rashin warkewa daga rauni da sauran su.

” Kiba, shan taba, shan giya, yawan shan kayan zaki, rashin cin ganyayakin da ake ci da kayan lambu na daga cikin abubuwan da ya kamata a kiyaye.

” Bincike ya nuna cewa a shekarar 2015 cutar ta yi ajalin mutane sama da miliyan 1.6 a duniya.”

Bayan haka ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa domin wayar da kan mutane da wuraren samun kula game da cutar ma’aikatar kiwon lafiya da wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun kafa kwamiti domin haka a Abuja.

Adewole ya ce kwamitin dake da taken ‘Diabetes Awareness and Care Project (DAC)’ za ta fara wayar da kan mutane a kan cutar a jihar Imo da babbar birnin tarayya Abuja.

” Mun kirkiro wannan dabara ne domin dakile yaduwar cutar a kasar nan

Share.

game da Author