Akalla wasu ruwa ya ci ruyukan wasu ‘yan bautar kasa su bakwai a jihar Taraba, tare da wasu biyu da ake zargin su ma sun mutu, amma ba a gano gawarwakin na su ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da sahihancin wannan labari.
‘Yan bautar kasar dai sun je yawon kurmiye ne a cikin ruwan Kogin Mayo-Selbe, wanda ke da mahada da Kogin Benuwai.
Su na cikin wanka ne sai wata igiyar ruwa ta malala musu daga kan wani tsauni inda nan take ruwa ya yi awon gaba da su zuwa cikin babbar kogin Benuwai.
Kwamishinan ‘Yan sandan Taraba, David Akinremi ya tabbatar wa PREMIUM TIMES faruwar wannan al’amari a yau da safe.
“Yan bautar kasar su 22 ne suka je wanka a cikin kogin, amma yayin da ruwan ya yi ambaliya daga saman wani tsauni, sai ya yi awon gaba da su.”
Akinremi yace al’amarin ya faru a Karamar Hukumar Gashaka, inda aka tura ‘yan bautar kasar su 22 su yi aiki.
Kafafen yada labarai da dama sun tabbatar da faruwan wannan hadari.
Hadarin ya tsaya a kan su ne bayan da aka hanzarta ceto wasu ‘yan bautar kasar, kafin ruwan ya yi nisa da su.