Gowon yayi kira da a saka masu dauke da cutar ‘Hepatitis’ a shirin Inshorar Lafiya ta Kasa

0

Tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya yi kira ga gwamnati da ta saka masu fama da cutar Hepatitis a shirin ta na Inshorar Lafiya ta Kasa, wato NHIS.

” Kamata ya yi mutane su gane mahimmancin sanin matsayin su game da cutar ta hanyar yin gwaji domin hakan ne zai taimaka wurin hana yaduwar cutar.

Bayanai sun nuna cewa binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi ya nuna cewa cutar ta kashe mutane akalla miliyan 1.32 a duniya.

Sannan a Najeriya mutane miliyan 20 zuwa 30 na dauke da cutar sannan da dama ba su da masaniyyar matsayinsu game da cutar.

A karshe Gowon ya yi kira ga gwamnati da ta kara wa fannin kiwon lafiya kason kudaden da take ware mata a cikin kasafin kudin kasa.

Share.

game da Author