Akwai akalla ‘yan Najeriya 116 da ke zaman bauta a Libya – Abike Dabiri

0

Mai Taimakawa ga Shugaban Kasa a Harkokin ‘yan Najeriya Mazauna wasu Kasashe, Abike Dabiri ta bayyana cewa akwai ‘yan Najeriya 116 da ke zaman bauta a sansanonin daban daban a kasar Libya.

Kakakin Yada Labaran ta ne Abdur-Rahman Balogun ya bayyana a cikin wata takarda da ya fitar a madadin ta, jiya Lahadi a Abuja.

Dabiri ta ce Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kasa-da-kasa kan kula da ‘yan gudun Hijira sun gano inda wannan sansanonin bautar da mutane su ke, kuma sun amince za su tattauna dawo da duk wanda ke son dawowa gida.

Ofishin Jakadancin Najeriya a Libya da ke birnin Tripoli ya gano wadannan ‘yan Najeriya da ke tsare a sansanin cibiyar bautar da bakake a Zawiya da ke Libya.

Dabiri ta ce tuni an kammala shirya bayanan da ake bukata na wadannan ‘yan Najeriya 116, kuma ba da dadewa ba za a maido su gida.

Sai dai kuma 24 daga cikin su sun bijire sun ce su fa sai sun tsallaka zuwa Turai ko a cikin buhun barkono ne, idan ana zuwa, to sai sun je.

Wannan kokarin ceto su ya taso ne bayan da aka fitar da wani bidiyo a ranar 8 Ga Yuli, inda aka nuno irin gallazawar da ake musu a sansanin.

Share.

game da Author