Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ta kwashe maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya su 34,978 a jigila 90 da jirage uku suka rika yi domin kai maniyyatan aikin Hajjin bana.
Hukumar aikin Hajjin ce ta bayyana haka a jiya Laraba. Ta ce an kwashe maniyyatan daga filayen jiragen sama daban-daban a kasar nan.
Daga nan kuma hukumar ta ce kamfanonin jirage uku ne suka yi wannan zirga-zirga, da suka hada da Max Air, Medview da kuma Flynas Air na kasar Saudiyya.
Ana sa ran za a kammala jigilar a ranar Juma’a mai zuwa.
Baya ga mahajjatan da suka tafi daga karkashin hukumar Alhazai, akwai kuma kimanin 20,000 da suka tafi a karkashin jirgin yawo, wato kamfanoni masu zaman kan su.
Za a fara aikin Hajji gadan-gadan a ranar Lahadi, inda mahajjata kimanin milyan biyu za su dunguma daga Makka su nufi Mina. Washegari zu zarce Arafat.
Idan sun yini a can, su dawo Mustalifa su kwana, da safe kuma su zarce su yi jifar Shaidan, su zarce cikin Makka a ranar Sallah kenan, a yi aski, a cike Harami a saka sabbin kaya. Da yamma kuma su koma Mina, inda za su kara yin kwanaki biyu sun a jifar Shaidan.
Daga nan za su dawo Makka, aikin Hajji ya kare kenan.