Likitoci sun gano sabuwar maganin hawan jini

0

Wasu likitoci a kasar Amurka sun gano sabuwar maganin ciwon hawan jini wanda aka kira ‘Triple pill’.

Likitocin sun bayyana cewa sun gano wannan magani ne a wata binciken da suka gudanar inda suka hada magungunan hawan jini kala uku wuri daya.

” Mun gano dabaran hada magungunan hawan jini kamar su medications telmisartan (20 mg), amlodipine (2.5 mg), and chlorthalidone (12.5 mg) zuwa kwaya daya. Sannan muka gwada ingancin maganin a jikin mutane 700 dake dauke da cutar.

” Sakamakon da muka samu ya faranta mana rai domin duk masu fama sun sami sauki bayan amfani da maganin Triple Pill.

Jagoran likitocin Ruth Webster ta bayyana cewa sun gudanar da wannan bincike ne domin rage matsalolin da likitoci kan yi fama da shi yayin da suke kula da masu hawan jini.

A karshe Ruth ta ce burin su shine likitoci da masu fama da wannan cutar su amince da wannan maganin sannan suna kokarin ganin yadda za su rage farashin sarrafa maganin.

Share.

game da Author