Mata ta roki kotu ta raba auren ta da mijin ta saboda yawan neman ta da yake yi

0

A yau Laraba ne kotun dake Iseyin jihar Oyo ta warware auren Baliki Oke da mijinta Arowolo bayan kuka da ta kai cewa yana matsa mata da yawan jima’I.

” Shekarun mu 7 da aure amma kuma abin sai kara gaba yake. Kullum dai aka hadu ayi harka. Ya kan dawo daga gona da rana tsaka don ya kwanta dani, bayan haka ya koma gona. Hakan bai hana shi nema na da dare kullum ne kuma.”

Baliki ta ce mijinta kan lakada mata duka a duk ranar da ta ki amince masa domin shi a ra’ayinsa sai ya kwana da mace sau shida a rana sannan yake gamsuwa.

Gogan naka kuwa bai musanta haka ba, Arowolo yace tabas yawan son kwana da mace ya zama masa matsala a rayuwa domin har ya nemi magani kan haka.

Arowolo ya roki kotu da kada ta raba auren su cewa ya yi alkawarin neman taimako akan matsalar da yake fama da shi.

Alkalin kotun Adelodun Raheem ya raba auren Baliki da Arowolo kan cewa Baliki da ‘yan uwan ta sun dage cewa ba za ta ci gaba da auren ba.

Share.

game da Author