An ceto mutane bakwai daga hannun mai safarar mutane a kan iyakar Katsina

0

Jami’in Kula da Shige da Ficen Najeriya sun cafke wata mata bayan sun ceto wasu mutane bakwai daga hannun ta.

An kama matar mai suna Asia Rita a Magama da ke kan iyakar Karamar Hukumar Jibiya da Jamhuriyar Nijar.

Shugaban Jami’an Shige da Fice na Katsina, Ajisefa Olusola, ya bayyana wa manema labarai cewa an kama ta ne tare da mutane bakwai kwanaki uku da suka wuce.

Kamar yadda ya yi bayani, wadanda aka samu din a hannun ta sun kama daga shekaru 11 zuwa shekaru 44. Sannan kuma ya ce mutane bakwai din da aka ceto daga hunnun Rita, shida mata ne, sai daya namiji.

Ya ce bincike ya nuna cewa wadanda aka ceto daga hannun Rita din duk su na dauke da takardun fita wajen Najeriya daga gari daya, duk kuwa da cewa dukkan su daga gari daban su ke, kuma ba ‘yan Jihar daya ba ne.

Rita ta na dauke da bizar iznin zama kasar Libya, kamar yadda fasfo din ta ya nuna, kuma ta na yawan shiga da fita kasar Libya a kai a kai.

Ya kara da cewa niyyar Rita shi ne ta yi safarar wadanda ta ke tare da su din har su bakwai zuwa cikin Jamhuriyar Nijar, daga can su tsallaka Libya. Daga Libya kuma su ketara cikin kasashen Turai.

A karshe ya ce za a dunguma a mika su hedikwata a Abuja, domin daukar matakin da ya fi dacewa kan wadda ake zargin.

Share.

game da Author