Da wuya a iya tantancewa, fayyacewa ko kuma sahihance asalin harshen Hausa da lokaci ko jinsi da al’ummar da suka fara yin amfani da shi. Sai dai kuma hakan bai hana manazarta, masana, masu bincike da kuma manyan malamai rika yin kirdado da kintacen kokarin gano asalin Hausa ba.
Harshen Hausa na daya daga cikin harsunan da ke yado, ba a nan Najeriya kadai ba, har ma a cikin kasashen Afrika ta Yamma da wasu kasashe da dama.
Ta ko wane fanni za a iya cewa Hausa ta samu karbuwa a duniya, idan aka yi la’akari da hanyoyin zamani na isar da sakonni, ilmantarwa da fadakarwa.
Harshen Hausa ya rika tumbatsa tare da samun karbuwa, idan aka yi la’akari da yadda Turawan mulkin mallaka suka rika amfani da shi wajen isar da sakonni da kuma mu’amala. Misali a zamanin Yakin Duniya na Farko, an rika amfani da harshen Hausa wajen isar da sakonni da mu’amala tsakanin sojojin da aka kwasa daga nan Arewa.
Ko a can baya, lokacin da Turawa suka shigo da kuma kafin zuwan Turawa, cinikayya da masu yawon fatauci daga kasar Hausa zuwa cikin wasu kasashe, sun taimaka wajen tumbatsar harshen Hausa a sassa daban-daban na Afrika.
HAUSAR BOKO A RUBUCE
Masana da daman a Harshen Hausa sun jaddada cewa Turawan Mulkin Mallaka da suka mamaye Arewacin Najeriya daga 1900 ne suka kirkira, ko kuma suka fara fito da rubutun Hausa na Boko.
An samu zakakuran Turawa da suka shigo Arewacin kasar nan, suka rika tattara kalmomi na Hausa, wannan a lokacin da rubutun ya fara kankama kenan.
Wani Baturen Ingila mai suna Bergery, ya buga kamus na Hausa zuwa Turanci, tun a cikin 1918, wanda ke kunshe da kalmomi kusan 39,000.
DAGA BAKIN MALAMAI: Farfesa Hambali Jinju
Marigayi Farfesa Hambali Jinju, mashahurin masanin Hausa kaga jamhuriyar Nijar ka ya shafe shekaru a Jami’ar Ahmaku Bello ta Zariya, a cikin littafin sa mai suna “Garkuwar Hausa ka Tafarkin Cigaba” ya na cewa,
“Zaurancen ra’ayin Hausawa ne cewa babu wani harshe a duniya ban da Larabci wanda ya fi Hausa daraja ko dadin ji, ba shi ma Larabcin saboda addinin musulunci ne kawai. Ko da yake Turanci ya yi kaka-gida a kasar Hausa musamman birane, wannan ra’ayin Hausawa bai sauya ba.
“A farkon wannan karni na1903 ne Turawa suka zo wa Hausawa da harsunan su (Ingilishi a Nijeriya, Faransanci a Nijar), suka tilasta musu su koye su daga (1903) zuwa (1960).
“A tsawon wannan lokaci Hausa ta zama marainiya maras gata. Makiyanta, Turawa da tsirarrun Afirkawa a zamanin mulkin mallaka suna yi mata dariya wai ba ta iya baza ilimin fasaha da kimiyya ba, amma a yau masu muguwar suka a da sun yi shiru sai dai kulle-kullen banza da makirci da ba za su fasa yi ba sai ran da dole ta zo musu kai-tsaye. Turawa sun shammaci Hausawa, amma duk da matsayin da harsunan ‘yan Ingilishi da Faransanci musamman daga karnonin tsakiya na Turai zuwa karni na 20.
“Ba mu taba samun shaidar cewa Hausa, kafin karni na 7, ta sami rubutu ba, amma mun san cewa sahabban Manzon Allah sun fito daga tsibirin Larabawa (Arabic Peninsula) sun bi ta Afirka ta Arewa sai Tumbutu. Lokacin da wadansu kamar su Ukba Ibn Nafi’i da jama’arsu, suka tunkaro zuwa gabas sun biyo ta kasar da yau ake kira Jamhuriyar Nijar a 666 inda suka soma yada addinin musulunci.
“Bayan karni na bakwai Abdulkarim Al-Maghili wanda ya rasu a 1504 ya ziyarci Nijar da Kano da Katsina yana ta yin wa’azi kuma ya na ta karantar da ‘yan kasa. A Katsina an yi waliyai biyu da ake girmamawa har kwanan gobe. Su ne Shehu Danmarina (da Larabci Ibn Alsabbagh) wanda ya rasu a 1655 da Danmasani wanda ainihin sunan sa shi ne Muhammad Albarnawi.
“Musulunci ya shigo Nijeriya a karni na 14. Daga wannan lokacin su waliyyi Danmarina aka sami tabbacin yin amfani da ajami saboda rubutattun wakokin Hausa an fara samunsu daga wadannan magabata ne. A kusan gaban kowanne gida, kafin zuwan mulkin mallaka, akwai makaranta. Wannan tsarin ilimi ya lalace sarai tun 1903, lokacin isowar Turawa kasar Hausa. Hausa ta na da kalmomi nata na asali wadanda yawancin su su na cikin Masaranci, harshen su Fir’auna. Ta kuma aro kalmomi da yawa daga wadansu harsunan Afirka ta yamma kamar Sanwayanci da Zabarmanci da Barbarci da Azbinanci da Fulatanci da Nufanci da kuma Yarbanci.”
GUDUMMAWAR JARIDU DA RADIYO
Masana da manazarta da dama sun yi makaloli dangane da Harshen Hausa. Ko ma dai me kenan, hanyar sadarwa musamman kafar yada labarai ta kara haifar da tumbatsar harshen Hausa a duniya.
Tun ma kafin shigowar radiyo ko kuma yawaitar sa a Arewacin Najeriya, jarida na daya daga cikin kafar da ta taimaka wajen yada harshen Hausa da kuma samar da karbuwar sa a sassa daban-daban.
An fara buga jaridar Hausa ta farko, wato GASKIYA TA FI KWABO a cikin 1938. Wannan kuma tabbas ya na nuna cewa tun a lokacin Harshen Hausa ya shiga gaban sauran harsunan Najeriya kenan.
Shigar da Harshen Hausa a kafafen yada labarai na kasashen Turai, Amurka da wasu kasashe na cikin wasu Nahiyoyi, ya nuna karfin sa da kuma irin yadda ya ke da tasiri ga isar da sako da ilmantarwa.
An bude Shashen Hausa na Radiyon BBC London, VOA, Jamus, Faran sa, China, Iran da sauran kasashe da dama. Kusan kasashen Afrika ta Yamma babu inda ba a magana da harshen Hausa.