Gwamnatin Kaduna ta tsawaita lokuttan zaman gida dole a unguwannin Kwaru- Unguwar Yero daga 7 Zuwa 7 na yamma kamar yadda yake ada zuwa awa 24 cur.
Kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ne ya fitar da wannan sanarwa inda ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin samar da tsaro a Unguwannin.
Idan ba a manta ba da yammacin Lahadi ne mutanen unguwan Malali, suka gamu da fushin wasu matasa da dauke da makamai inda suka far wa mutanen unguwar da sare-sare.
Mutanen unguwar da suka tattauna da wakilin PREMIUM TIMES sun fadi cewa matasan sun shigo unguwar daukar fansa daya daga cikin dan uwan su da aka kashe a rikicin Unguwar Yero da Kwaru ne.
Umma Dauda ta sanar wa PREMIUM TIMES cewa sun dan shiga cikin tashin hankali, kafin zuwan jami’an tsaro.
” Jami’an tsaro ne suka kawo mana dauki domin kuwa matasan da muke ganin sun shigo unguwar don daukan fansa ne suna dauke ne da zaratan makamai a hannun su.
Wani mazaunin unguwar ya furta cewa ya ga wasu mutane biyu kwance cikin jini a lokacin da ake guje-guje.
Duk da cewa mun nemi ji daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna hakan a ci tura, sai dai wani shugaban ‘Yan banga da ke zaune a unguwar ya shaida wa wakilin mu cewa yanzu komai ya lafa, har ma yana ganin an dan yi kame a unguwan.