An saki matan Faston da aka kashe aka sace ta a Kaduna

0

Masu garkuwa da mutane sun saki matar Faston cocin Baptist dake Igabi jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan Kaduna Yakubu Sabo ya bayyana cewa an saki wannan mata ne a wuni wuri cikin dare.

Idan ba a manta ba masu garkuwa sun kashe mijin Talatu Akushi, Hosea Akushi da shine faston cocin Nasara Baptist dake Igabi, jihar Kaduna sannan suka tafi da ita.

Talatu ta yi kwanaki shida tsare a hannun masu garkuwan.

Sai dai wani makusancin Talatu ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sai da aka biya masu garkuwan Naira 500,000 kafin suka sake ta.

Ba mu iya tantance tabbacin haka ba.

Yanzu dai an garzaya da Talatu zuwa wani asibiti domin duba lafiyar ta.

Share.

game da Author