Shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA) Francis Faduyile ya yi kira ga ‘yan siyasar kasar nan da su tsuke bakunan su wajen fadin kalaman da zai iya tada zaune tsaye a kasar nan.
Faduyile ya yi wannan kira ne ranar Juma’a inda ya bayyana cewa fadin munanan kalamai musamman a wannan lokaci da zaben 2019 ya kunno kai zai iya yi wa kasa illa matuka.
” Najeriya za ta iya fadawa cikin halin rashin zaman lafiya a dalilin irin wadannan kalamai sannan abin takaici shine talakawa musamman mata da yara ne za su fi fadawa cikin matsala.
” Kuma fannin kiwon lafiya ma za ta fada cikin irin wannan matsala.
Kungiyar ta yi kira ga ‘yan Najeriya musamman matasa da su zama ma su yin biyayya ga doka.