Mahaifin Amina da maza hudu suka yi wa fyade ya daukaka kara a Jos

0

Alhasan Abdullahi mahaifin Amina Ismail dake fama da tabuwan hankali ya daukaka kara a babban kotun dake Jos jihar Filato inda yake neman kotu da ta kwato wa ‘yar sa hakkin ta.

Abdullahi ya bayyana cewa Dahiru Maishayi, Ibrahim Aliyu, Shu’aibu Umar, Illa Isma’il da Mallam Alajeje sun yi wa ‘yar sa mai suna Amina Ismail fyade, da a dalilin haka ta dauki ciki har ta haifi ‘ya mace.

” Mu dai mazaunan Unguwar Rogo ne a karamar hukumar Jos ta arewa sannan wadannan mazajen sun yi wa ‘ya ta fyade ranar 16.

Ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ta kama wadannan maza ranar 17 sannan ta tsare sun na tsawon makonin biyu bayan gurfanar da su da aka yi a kotun a garin Jos.

Abdullahi ya ce sai dai kafin a kai ga ranar yanke wa wadannan maza hukunci rundunar ‘yan sanda ta sake su.

” Da muke kotu ban ji lokacin da alkali ya bada belin su ba domin hannan ce in biya kudin motar da za a kaisu kurkuku kuma na biya.

A karshe kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Luka Ayedoo ya tabbatar cewa an saki wadannan mutanen dake tsare.

Ya bayyana cewa sun sami umurni daga kotun dake Jos cewa wadannan maza sun cika duk sharaddan belin da aka basu shine ya sa aka sake su.

Share.

game da Author