Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa baki daga masarautar Daura da suka ziyarce shi cewa aikin noma na daga cikin ayyukan da gwamnatin satafi maida hankali a kai tun bayan hawan ta a 2019.
Bayan haka ya yi tsokaci game da takawa da yayi daga masallacin idi zuwa gida da yake da tsawon mita 800.
” Ni ban taka daga masallacin Idi zuwa gida don in burge kowa ba. Tun bayan da na fito daga masallaci sai naga dandazon jama’a suna ta miko gaisuwa.
” Da na ga haka sai na fito domin in yi amfani da wannan dama mu gaggaisa da jama’a. Da yawa cikin su na son su ganni amma basu sami wannan dama ba. Wannan shine babban dalilin da ya sa na fito na taka zuwa gida.”
Bayan haka ya sanar wa bakin sa cewa za a sake fasalin raba basuka ga kananan manoma domin inganta ayyukan noman su.
” Dole ne mu iya samar wa kananan manoma basuka da ba sai sun ajiye wani abu ba a matsayin jingina. Wannan shiri shine muke so mu ga ya tabbata.
Daya daga cikin bakin Buhari, Maiaduwa ya roki Buhari da ya amince ya amsa gaiyatar su, kan shirin gangami da masarautar Daura ke shirya masa da zarar an daga dokar hana kamfen.