An rantsar da sabon shugaban hukumar SSS, Matthew Seiyefa

0

Bayan korar shugaban hukumar tsaro na SSS Lawal Daura da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo yayi an rantsar da sabon shugaba na riko, Matthew Seiyefa.

Seiyefa ne babban darekta da ke gaba da kowa bayan Lawal Daura a hukumar.

Sai dai kuma har yanzu ba a san inda Lawal Daura ya ke tun bayan sanar da korar sa da akayi.

Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya fatattaki shugaban hukumar DSS Lawal Daura.

A wasikar sallamar da aka mika masa, an umurce shi da ya mika ragamar mulkin ga babban darekta a ke hukumar.

Wannan kora da aka yi wa Lawal Daura dai ya na da nasaba yadda jami’an tsaro na DSS suka far wa majalisar kasa da safiyar Talata.

Kafin a kori Lawal Daura sai da mataimakin shugaban Kasa ya umarce shi da sufeto janar su bayyana a ofishin sa.

Jim kadan bayan sun bayyana ne fa Osinbajo ya fatattake shi.

Share.

game da Author