Tsohon shugaban Hukumar bada agajin gaggawa ta Kasa NEMA, Sani Sidi ya mika takardar yin takarar gwamnan jihar Kaduna.
Sani Sidi ya mika takardar ne a ofishin Jam’iyyar PDP dake Kaduna.
A jawabin sa Sidi ya bayyana cewa ya fito takarar gwamnan Jihar Kaduna ne domin ya dawo wa jihar da martabar ta da aka santa da shi.
” Na zo wannan ofishi ne domin in mika takardar muradin yin takarar gwamnan jihar Kaduna a Inuwar Jam’iyyar PDP. Na yanke wannnan shawara ne domin nuna godiya ta ga jama’ar jihar Kaduna game da irin gudunmuwar da suka bani a tsawon ayyukan da nayi a rayuwa ta.
” Lokaci yayi da zan saka wa mutanen jihar Kaduna bisa ga abin da suka yi mini. Babban haryar da naga ya fi dacewa kuwa shine ta wannan hanya.