Hedikwatar APC tayi fatali da dakatar da Shehu Sani da jam’iyyar ta yi a Kaduna

0

Hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa ta yi fatali da dakatar da Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani da jam’iyyar tayi a Kaduna cewa bata san da haka.

Kakakin jam’iyyar APC na kasa Yekini Nabena ne ya sanar da haka a wata shimfidaddiyar takarda da ta fito daga hedikwatar jam’iyyar ta kasa.

” Jam’iyyar APC ta kasa ta duba wannan wasika ta dakatar da Sanata Shehu Sani, sannan ta aika wa reshen jam’iyyar a Kaduna da ta gargadi masu yin irin wannan shiga sharo ba shanun. Sanata Shehu Sani na nan daram dan jam’iyyar APC da jam’iyyar ke alfahari da saboda haka jam’iyya ba ta san wannan magana ba na dakatar da shi ba.

” Idan ba a manta ba, sanata Shehu Sani ya ki bin a yarin masu komawa jam’iyyar PDP ne saboda kokarin sasanta wadanda ba sa ga maciji da juna a jam’iyyar.” Cewar Yekini.

Share.

game da Author