Tsohon gwamnan jihar AkwaIbom, Godswill Akpabio ya kammala shiri tsaf don canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Wani hadimin Buhari Okoi Obono-Obla, ne ya bayyana wa PREMIUM TIMES haka, sannan ya bamu tabbacin mu fadi wa kowa haka.
Obla ya ce shigowar Akpabio APC zai canza alkiblar siyasar jihar AkwaIbom.
Wannan zance dai ya shammaci ‘yan siyasa da yawa a Najeriya, domin kuwa kowa ya san Akpabio mutum ne da ke nuna adawar sa karara da jam’iyyar APC a baya.
Bayan haka kuma Akpabio ya garzaya kasar Britaniya, inda yayi ganawa ta musamman da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Mai taimaka wa shugaba Muhammadu Buhari kan harkar sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmed ne ya sanar da haka a shafin sa na tiwita.
Discussion about this post