Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, ya fada a yau Juma’a cewa jami’an EFCC sun amince da dakatar da yi masa tambayoyi a ranar Talata, bayan da ya shaida wa matambayan sa cewa “ba ya jin dadin jikin sa.”
An tambaye shi ne a kan zargin ya mallaki wasu fankama-fankaman kadarori da kuma hannun sa a cikin wasu harkalloli.
An fara yi masa tambayoyin ne a ranar Talata da safe, har zuwa faduwar rana.
An sallame shi ya tafi gida a bisa ba shi belin kan sa da kan sa, da nufin ya koma washegari Laraba a ci gaba da yi masa tambayoyi.
Duk da ya koma ofishin EFCC a washegari Laraba da safe, sai nan da nan ya nemi a bar shi ya tuntubi likitan sa, saboda rashin lafiyar sa ta sake bijirowa tun a cikin dare ranar Talata.
Haka kakakin yada labaran sa, ya bayyana wa PREMIUM TIMES.
Uche Anichukwu ya ce karya ne rahotannin da wasu jaridu suka rika yadawa cewa wai rubdugun tambayoyin da aka rika yi wa Ekweremadu ne suka sa nukurkusar masa da jiki, har ya rafke.
“Babu wasu rubdugun tambayoyi da aka yi wa Ekweremadu a ranar Laraba ko guda daya, ballantana a ce wai har sun rafkar da shi. Masu kirkirar karairayi ne kawai suka rika yada ji-ta-jitar.” Inji Anichukwu.
Ya ce EFCC sun amince Ekweremadu ya je ya nemi lafiyar sa, daga baya kuma za a sake sa wata rana.