Ka sauka ko ka yi shirin daukar dala ba gammo – Gargadin Sanata Adamu ga Saraki

0

Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya tsokano tsuliyar dodo, tunda ya kuskura ya koma PDP, don haka ya jira saurari shan radadin sakamakon abin da ya shuka.

Saraki da Adamu aminan juna ne na kut da kut a can baya, amma batun mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya ne ya sa su biyun suka raba hanya.

Tun da farko cikin wannan makon ne Saraki ya ragargaji Sanata Adamu, inda ya kira shi mayaudari kuma makaryaci.

A yau Juma’a shi kuma Adamu ya rama raddin da Saraki ya yi masa, ya na mai cewa da Saraki ya yi tunani irin tuggu da kutuiguilar siyasa da kuma karankatakaliyar neman matsayi a mulkin Najeriya, to da ya rika takawa sannu a hankali.

Domin a wannan lokacin dai ya dora kafar sa kan bawon ayaba mai santsi, wanda ya na ji ya na gani santsi zai kwashe shi ya yi masa mummunan kayen da bai taba tunani ba.

“Ba fa burga ce kawai na ke yi ba, ai Saraki ya buga babban kuskure. Kuma shi ne nan gaba zai bada labarin irin sammatsin da duniya ta yi masa”

Daga nan sai Sanata Adamu ya roki Saraki da ya shafa wa kan sa lafiya, ya sauka daga mukamin shugabanin majalisar dattawa.

“Ko dai ya shafa wa kan sa lafiya ya sauka daga kujerar shugabancin majalisa, ko kuma ya dandana kudar gatarin sa da kan sa.”

Adamu wanda a majalisar dattawa shi ne shugaban masu goyon bayan Buhari, ya sha alwashin cewa ai tunda dai har Saraki ya kuskura ya fice daga APC, to kuwa ya hada kan sa da tsugune-tashi.

“Mu abin da mu ka so shi ne idan za su fice, to su fice salum-alum hannu biyu. Amma bai yiwuwa su fice daga APC kuma su shiga PDP dauke da shugabanin majalisa, wanda APC aka ba shugabancin ba wai Saraki aka ba kankin kan sa ba.

Sai dai kuma ana ganin zai yi wuya a iya tsige Saraki, domin ya na da magoya baya a bangaren APC da kuma uwa uba jam’iyyar PDP inda ya koma.

Sannan kuma wata matsalar ita ce sai kashi biyu bisa uku ne na sanatocin za su iya tsige shi, kamar yadda doka ta tanadar.

Share.

game da Author