Ba ni da niyyar barin APC – Gwamna Bello na jihar Neja

0

Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Bello, ya ce ko da rana daya bai taba yin tunani ko niyyar ficewa daga jam’iyyar APC ba.

Gwmanan ya yi wannan bayani ne ganin yadda wasu ‘yan majalisa da gwamnoni suka fara ficewa daga APC su na komawa jam’iyyar PDP.

A cikin wani jawabi rubutacce da kakakin yada labaran sa Jibrin Ndace ya sa wa hannu, gwamna Bello ya ce har yanzu ya nan mubayi’ar siyasar na a hannun Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce shi yanzu a APC ba mamba kadai ba ne, ya na ma daya daga cikin manyan jijiyoyin jam’iyyar, domin a cewar sa, ita kadai ce jam’iyyar da za ta iya ceto kasar nan daga barnar da aka yi a baya.

Ya kara da buga misalan da ya ce gwamnatin APC ta samar da ci gaba a cikin shekaru uku a bangaren noma, lafiya, ilmi, zaman lafiya, tsaro, matasa da mata da kuma samar da ababen more rayuwa musamman a jihar Neja.

Ya ci gaba da jinjina wa kan sa da gwamnatin Buhari wajen wasu ayyukan da ya ce gwamnatin baya ta fara ta watsar, amma wannan gwamnati ta kammala su.

Share.

game da Author