RASHA 2018: Brazil ta tsira da mutuncin ta, Mexico ta zargi alkalin wasa

0

Duk da cewa Brazil ta zuba kwallye biyu a ragar Mexico, hakan bai nuna bajintar kungiyar kwallon kafar kasar sosai ba, sai dai kawai a ce ta tsira da mutuncin ta zuwa wasa na ‘kwata-final’ kawai.

Dan wasan PSG, Neymar ne ya fara jefa kwallo a daidai minti na 51, shi kuma Firminho na Liverpool ya antaya kwallo ta biyu.

Sai dai kuma mai horas da ‘yan wasan Mexico, Osorio, ya yi tir da alkalin wasa inda ya ce an nuna wa ‘yan wasan sa bambanci karara.

Brazil ta samu hayewa, yayin da sauran mashahuran kasashen da ake tunanin cewa a tsakanin su ne za a yi rububin damke kofin duniya, wato Germany, Spain, Portugal da Spain, duk an kora su zuwa gida.

Ana dai ci gaba da ganin wallen alkalan wasa yayin da dimbin masu kallo ke fadar ra’ayoyin su cewa su na lalata wasan kwallo, ta hanyar busar da ba ta dace ba kwata-kwata.

A wasan Spain da Rasha, Spain ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida har sau biyu, amma ba a ba ta ba, kamar irin yadda aka yi wa Najeiya a wasan ta da Ajantina.

Sai dai kuma abin mamaki, kwallo ta dira kan hannun dan wasan Spain, Gerard Pique, kuma ta baya, bai ma san ta dira ba, amma alkalin wasa ya hura bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Share.

game da Author