Dalilin zanga-zangar ‘yan sanda a Maiduguri –Kakakin su

0

Hukumar Tsaron ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa jami’an ‘yan sandan da hawo titi a Maiduguri, ba zanga-zanga suke yi ba, su na dai nuna damuwar su ce kawai game da jinkirin biyan su alawus-alawus da ba a yi ba kawai.

Kakakin yada labaran ‘yan sanda na kasa, Jimoh Moshood ne ya bayyana haka, tare da cewa kuma ba jami’an ‘Operation Lafiya Dole’ ba ne, da aka tura fada da Boko Haram.

Moshood ya ce tuni har Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan, Ibrahim Idris ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar Barno da ya gaggauta magance dalilin da ya sa aka samu jinkirin biyan su alawus din na su.

Ya kara tabbatar da cewa, tunda dai an rigaya an sa wa kasafin kudi hannu, to ba a wani ba ta lokaci ba za a gaggauata biyan kowa dukkan hakkokin su na alawus din su da ba a biya su ba.

Ya kuma umarci kwamishinan ‘yan sandan Mobal da ya gaggauta kai ziyara a jihar Barno da kuma sauran jihohin Arewa maso Gabas domin duba jami’an ‘yan sanda da ke ayyuka na musamman a can.

An kuma yi kira ga al’ummar jihar Barno da su ci gaba da gudanar da harkokin su lami lafiya, babu wata barazana.

Share.

game da Author