Ni din nan na kulla zumuntar siyasa tsakanin Buhari da Tinubu, duk da ya kyamaci haka – Buba Galadima

0

Shugaban R-APC, Buba Galadima, ya bayyana cewa shi ne silar hadawa da kulla kawancen siyasa tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

Cikin wata zazzafar tattaunawa da Galadima ya yi da Mujallar Interview, ya ce sai da ya sha wahala kafin Buhari ya amince da shawarar shi Buba Galadima din cewa ya kamata ya saurari Tinubu, da kuma jam’iyyar sa, ACN.

A wannan lokacin da Buba ke magana, Buhari ya na CPC, shi kuma Tinubu ya na ACN.

“Buhari ya yi kememe ya ce shi bai yarda a kulla kawancen siyasa da Tinubu da ACN ba, amma haka. Amma dai ba zan ce komai ba. Ya rage ga Buhari ya fito ya karyata ni. Haka na zauna na tsara komai hatta yarjejeniyar da samar da Osinbajo a matsayin mataimakin shugaban kasa, duk ni na tsara ta.”

Buba ya ci gaba da cewa ba don ya yi haka ba, da sunan wani can daban Buhari zai mika ga INEC a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, ba Osinbajo ba.

Galadima ya shaida wa mujallar Interview cewa nan gaba kadan zai rubuta wa Buhari wata budaddiyar wasika, wadda bayan fitowar ta shi kan sa Buhari zai san cewa ya ma fadi zaben 2019 ya gama.

“Idan Buhari a Daura ya ke, ya na can a zaune ya na kiwon shanun sa, to ba zan damu da sukar sa ba. Amma tunda shi ne shugaban Najeriya kuma ba ya yin abin da ya kamata, dole in yi magana.

Share.

game da Author