Na makale a kololuwar bishiya na tsawon awa 11 – Dino Melaye

0

Sanata da ke wakiltar Kogi ta Yamma Dino Melaye ya bayyana yadda ya tsira daga fafurar da wasu ‘yan taratsi suka kai masa a hanyar Abuja zuwa Lokoja a makon da ya gabata.

A doguwar hira da ya yi da PREMIUM TIMES yace wasu motoci uku ne suka afka gaban sa a hanyar sa ta zuwa Lokoja domin amsa gayyatar Kotu.

” Ina tafiya na salin-alin sai kawai wasu motoci uku suka shigo gabana da ya sa dole na taka burki na tsaya.

” Tsaya wa na ke da wuya sai suka nemi su bude mini wuta da bindigogi, amma kuma mota ta bindiga baya huda ta. Daga nan sai suka fara ihu suna cewa ‘mu kona shi a cikin motar, mu kona shi a motar.’ Sai suka tsallaka titi neman taya da itatuwa domin su babbake ni a cikin motar.

” Ana haka ne fa ni kuma na yi wuf na fito daga cikin motar na arce cikin kungurmin daji, suka ko biyo ni da gudun tsiya, amma kafin su tadda ni na dare wata itaciya na yi shiru abina.

” Ina saman wannan bishiya sai na hango su sun wuce ni da gudu suna nema na. Na yi shiru tsit sai naga sun dawo sun koma da baya.

Dino ya kara da cewa a haka ne ya makale a can saman bishiyar har tsawon awa 11. Sai da ya tabbatar sun tafi sannan ya sakko ya kama gaban sa.

Ya ce zai iya gane motocin da suka bishi, domin ya ga wadannan motoci a kotu a Abuja ranar Laraban makon da ta gabata.

” Ina tabbatar muku da cewa wannan shiri ne da hadin bakin ‘yan sanda. Kuma idan ma an kashe ni, gobe irina 100 za su bayyana don ci gaba da gwagwarmaya.

“Ba zan gaji da fadin aibin mulkin Buhari ba”

Dino yace ya nemi a samar masa da jami’an tsaro na ‘Civil Defence’ amma an ki ba shi sabo da fin karfi.

” Kiri-kiri a matsayina na sanata a Najeriya amma an hanani jami’an tsaron da za su rika kula da ni, balle kuma sauran ‘yan Najeriya.”

Dino dai ya fadi cewa wannan abu ya faru ne a gaba kadan da garin Gwagwalada a hanyar sa ta zuwa Lokoja daga Abuja.

Share.

game da Author