Kafin Shekau, Mahara, Sauro da Kanjamau Su Kassara Najeriya, Daga Ashafa Murnai

0

A yau an wayi gari a Najeriya an saba da kisa da zubar da jianainai, kamar yadda aka saba da bukukuwan aurarraki da ko yawan haihuwa. Don an kashe mutum 20, 30 zuwa 50, abin ya fara zama jiki, tun daga gwamnati har su mazauna jihohin da tashe-tashen hankulan ke faruwa, sun daina tayar da hankulan su.

Daga 2009 zuwa yau, nau’o’in kashe-kashen da ke wakana a kasar nan akasari duk ba mu san sub a, sai dai a tarihi mu ke karanta su a litattafai. Tafiya ta yi tafiya, muka rika kallon wasannin kwaikwayon wadannan kashe-kashe a gidajen silima zuwa cikin talbijin.

Tun bayan Maitatsine, ba mu san maganar zubar da jini bagatatan ba, sai fa idan an samu sabanin rikicin addini ya barke.

Yayin da bala’in Boko Haram ya kunno kai, sai mu ka rika tuna labaran da muke karanatawa a cikin littattafan Hausa da suka kunshi labarin Mai Asagiri, wani dan samame da aka taba yi a Daular Bano, sai kuma labarin wani gogarman samame da ya danno daga Daular Sudan, ya wo yamma da yaki, har sai da ya ci Daular Barno, ya kafa na sa mulkin. Ina nufin labarin dan samame Rabeh.

Tun matsalar Boko Haram ba ta kau ba, mun samu kam mu cikin wani mummunan tashin hankali, na barkowar ‘yan samame a wasu yankunan jihohin Arewacin kasar nan, musamman a yankin Birnin Gwari, Katsina da kuma Zamafara da Sokoto.

Samamen nan ya yi muni a shekarun baya a Katsina, amma yanzu a Birnin Gwari da Sokoto suke yi, sai kuma uwa-uba jihar Zamfara, wadda idan ba a yi aune ba, za su iya kwace jihar.

‘Yan samame na zamanin da can da dare ko da rana suke bi su yi wa kauye tsinke, sun kwashi matan aure da ‘yan mata, su kwashi dukiya da dabbobi masu tarin yawa, su karkashe mazan garin ko kauye, sannan kuma su banka wa kauyen wuta.

Wannan salon a fashin dukiya ko kamen bayi da ake kira samame, yanzu ya mamaye jihar Zamfara, tamkar yadda Boko Haram ya addabi Arewa maso Gabas. Sai dai su ‘yan samame, ba su kai ga fara amfani da bama-bamai ba. Kuma ba mu fatan abin ya kai ga wannan munin.

A yau Lahadi, jaridar Vanguard ta rubuto cewa Najeriya ta kashe naira tiriliyan 7 a cikin shekara 11 a fannin tsaro. Ni kuma sai na ke ganin shin wa aka tsare da wadannan makudan kudaden? Ba dai ‘yan Najeriya ba. Domin a tarihin Najeriya, tun bayan Yakin Basasa ba a kashe mutane ba kamar cikin wadannan shekaru 11 wadanda aka fi kashe kudaden tsaro cikin su.

Idan kashe kudaden da aka yi kan tsaro sun yi tasiri sosai, ya kamata a ce Boko Haram ko da sun kai yawan kudan zuma an kakkabe su kowa ya huta. Don me kashe-kashen da ake yi a Zamfara ya ke wasa sabon lale a yanzu?

Baya ga Boko Haram da samame, wani yaki da har yau ya gagara a yi wa nasara a Najeriya shi ne yaki da sauro, ko zazzabin ciwon sauro, ko kuma duka biyu. A duk shekara, baya ga makudan bilyoyin da Najeriya ke kashewa, Majlisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai, kungiyoyi irin su USAID da sauran suna tula wa kasar nan bilyoyin nairorin yaki da sauro da zazzabin cizon sauro. Amma har yau babu alamar yin galaba ga wannan dan karami kwaro, wanda idan ka dunkule shi wuri daya bai kai kwarar dawa girma ba.

Kullum kashe wa sauro kudi ake yi, shi ma kisa ya ke yi. yadda ake yin yakin katilan-makatulan tsakanin sojoji da Boko Haram, haka ake katilan makatulan tsakanin gwamnati da sauro. Gwamnati na kashe bilyoyi kan sauro da zazzabin sa, shi kuma aniya ya ke yi ya na kashe kananan yara da manya duka.

Sai kuma cutar kanjamau, wadda a farkon shigowar ta Najeriya, har an ma fi tsoron ta fiye da mutuwar ita kan ta. Sannu a hankali ita ma sai ta zama jiki, saboda ita ma hanya ce wadda ake kusanta domin a rika kashe mata makudan bilyoyi. Yayin da ake kashe mata bilyoyi, a lokacin ne kuma ta fi kara ta’azzara? Shin mene ne dalili?

Wani rahoto da aka fitar ranar Juma’a, ya nuna cewa a kowace rana mutum dubu shida na kamuwa da cutar a duniya.

Tambaya ta a nan, me ya sa duk abin da aka fi kashe wa kudi, kuma a lokacin ne ma ya fi yi mana barna, illa da lahani? Ku dubi Boko Haram. Ku dubi samame. Ku dubi sauro, kuma ku dubi kanjamau! Me ya sa?

Share.

game da Author