Gwamnan Jihar Yobe Ibrahim Gaidam, ya ce jihar ta kashe naira bilyan 9 wajen samar da tsaftataccen ruwan sha a cikin shekara bakwai.
Gaidam ya yi wannan jawabin ne a wurin bude taron kara wa juna sani da gwamnatin jihar ta shirya wa mambobin Majalisar Dokoki na Yobe.
An kaddamar da taron ne jiya a Kano, inda Kwamishinan Kwamishinan Ilmi na jihar Muhammad Lami ya wakilci gwamnan.
Ya kara da cewa an shirya taron ne da hadin guiwa da Bankin Raya Kasashen Afrika mai kula da samar da ingantaccen ruwan sha a karkarar Afrika.
Gwamnan ya ce an shirya taron domin ilmantar da ‘yan majalisar dokokin jihar dangane dokokin da za a kafa kan tsarin ruwan sha a jihar.
Ya ce Hukumar Killace Kididdiga ta Kasa ta ce an samu ci gaba da kashi 75 bisa 100 a jihar a fannin inganta ruwan sha.