Gwaman Jihar Benuwai Samuel Ortom ya canza sheka daga jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP a yau Laraba.
Kakakin gwamna Ortom Terver Akase ya tabbatar wa PREMIUM TIMES haka ta wayar tarho.
Ba tun yanzu ba ake ta sauraren jin haka daga gwamna Ortom domin kuwa duk alamu sun bayyana cewa gwamnan yana gab da ya canza sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP tun ba yanzu ba,
A makon da ya gabata ne gwamna Ortom ya bayyana wa ‘yan Najeriya cewa jam’iyyar APC ta bashi jan kati na ya fice daga jam’iyyar.
A yau dai karau domin ya fice kwata-kwata.
Discussion about this post