Fadar Shugaba Muhammadu Buhari ta karyata zargin hannun da ake cewa ta na da shi wajen tura jami’an tsaro su mamaye gidajen Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Mataimakin sa Ike Ekweremadu.
A cikin wata takarda da Kakakin Yada Labaran Buhari, Garba Shehu ya saka wa hannu, fadar ta ce, “abin mamaki da al’ajabi shi ne yadda ake kama masara karfi ana bincika idan sun yi laifi, ba a kuka ko zargin gwamnati, amma duk ranar da aka kama wani babba, to za a dangata abin da ramuwar-gayya ko bi-ta-da-kulli.”
Ya ce abin ya yi muni ta yadda ake zargin fadar shugaban kasa wajen nuna ra’ayin siyasa kan wasu manyan kasar nan da jami’an tsaro ke bincika.
“Shugaban kasa ba ya shiga sha’anin jami’an tsaron kasar nan, saboda cin gashin kan su ne suke ci.”
“Shin sai yaushe ne za mu ci gaba idan za a rika kallon rashin kyautawa ko zargin siyasa a harkokin binciken wasu manya? Ai babu wanda ya fi karfin doka.”
“To abin da ya faru jiya dai dokar kasa ce ta yi aikin ta, kuma babu ruwan fadar shugaban kasa.”
“Abin da kowa ya sani shi ne Buhari ba zai zura wa jami’an tsaro suka karya doka su na yin yadda suka ga dama ba. Amma kuma ba zai yi musu katsalandan a cikin ayyukan su ba, ko kadan.
“Sannan tabbas ya ba su kwarin guiwar cewa komai girman mutum, in dai doka ta ce za a iya bincikar sa, to a bincike shi idan ana zargin sa da aikata wani laifi.”
Wadannan bayanai sun biyo korafe-korafen da suka rika biyo baya cewa fadar na amfani da jami’an tsaro wajen musguna wa wasu, sannan kuma jami’an su na kauda kai daga bincikar laifukan wasu majibin ta gwamnatin.