Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa wata kungiyar Dattawan Arewa da kuma wasu daidaikun da ke korafi da mulkin Muhammadu Buhari, duk kukan munafurci ne suke yi.
Kakakin Yada Labaran Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka a yau Juma’a.
“Wadannan dattawa su na korafin cewa wai mulkin Buhari ya maida yankin su saniyar-waye.
“Sun ce wai ba a cin moriyar raba albarkatun tattalin arzikin kasar nan daidai da na su yankin.
“Amma abin na su duk kukan munafurci ne kawai. Saboda sun ga zaben 2019 ya karato kuma sun ga alamomin nasara ga jam’iyyar APC mai mulki.”
Cikin makon da ya gabata ne Kungiyar Dattawan Arewa da wasu daidaikun dattawan Tsakiyar Arewa suka zargi Buhari da rashin iya mulki.
Sun fitar da sanarwar yadda gwamnatin ba ta tabuka komai wajen matsalar tsaro, ganin yadda kashe-kashe ke kara tsananta a fadin kasar nan.
Sai dai kuma Shehu ya ce rundunonin sojojin kasar nan da aka girke a yankuna da dama su na taka rawa sosai wajen kokarin dakile ta’addanci da fadace-fadacen makiyaya da manoma.