Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna ta bayyana cewa tun ranar Talatar da ta wuce
ne jiga-jigan jam’iyyar suka gana da ‘yan takarar gwamnan jihar a PDP domin a yi maslaha a tsakanin su su amince da dan takara daya.
Daya daga cikin ‘yan takarar Jaafaru Sa’ad ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Kaduna cewa jam’iyyar ta gana da ‘yan takarar sannan ta nemi da suyi shawara a tsakanin su.
” Dukkan mu ‘yan takarar gwamnan jihar mu 8 mun cancanta a dalilin haka ya sa jam’iyyar ta roke mu da muje a tsakanin mu mu fidda dan takara guda da zai karbu a Jam’iyyar da mutanen jihar Kaduna domin fafatawa da duk wanda jam’iyyar APC zata tsayar.
” A ganina hakan ya zama dole domin ba wai kawai ga jam’iyyar mu ba har ma ko don mutanen jihar Kaduna.
” Dukkan mu ‘yan takara mu 8 mun halarci wannan taro banda Isah Ashiru da ya aiko da wakili.” Inji Jaafaru.
Sakataren jam’iyyar Ibrahim Wusono yayi karin bayani kan wannan shawara da jam’iyyar ta dauka.
” Hakan ne muke gani mafita a garemu, mu tsaida amintaccen dan takara guda daya wanda zai karbu a jihar, domin burin mu shine mu tunkari zaben 2019 babu mishkila.
” Sai dai kuma idan har hakan bai yiwu ba toh zamu yi zabe a tsakanin su domin fidda dan takara daya tal. Ko da yake hakan bai hana wani ya fito daga baya ba.
” Abinda za mu shawar ce shi yayi shine ya je su sasanta tsakanin su da wanda muka zaba, Idan kuma bai amince ba sai ayi zaben fidda gwani.
” Ina kira ga sauran jihohin kasar nan da su bi irin wannan kokari da muke yi a jihar kaduna har da kasa baki daya domin samun nasara a 2019.