2019: Atiku zai kaddamar da takarar shugaban kasa a Yola

0

Tsohon Shugaban Kasa Atiku Abubakar zai kaddamar da takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a yau Asabar.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sa, ta bayyana cewa Atiku ya yanke cewa zai fito takara ne bayan ya yi yawon tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da kuma ita kan ta jam’iyyar.

A yau ne zai tsaya a gaban dimbin magoya bayan sa a Yola, babban birnin jihar Adamawa da rana domin ya yi amfani da damar hasalar da wasu suka yi da wannan gwamnati, har ya yi kokarin samun goyon bayan biyan doguwar bukatar da ya dade shekara da shekaru ya na nema.

Atiku wanda tsohon kwastan ne, ya fara sha’awar tsayawa takarar shugabancin kasa tun cikin 1993, a karkashin SDP, ya yi wa Obasanjo mataimakin shugaban kasa a zaben 1999, sannan kuma sake neman takara ba sau daya ba a wasu jam’iyyu.

Sanarwar ta ce da zaran ya kaddamar da takarar ta sa, Atiku zai kuma bayyana manufofin sa da kuma kudirorin sa idan har an zabe shi ya zama shugaban kasa.

“Kadan daga cikin su akwai tattalin arziki, sake fasalin Najeriya, ilmi, kiwon lafiya, noma, inganta rayuwar mata da kuma wasu da dama.

A 2007 Atiku yayi takara da Umaru Yar’Adua, ya yi da Goodluck Jonathan a 2011, sannan a 2015 ya yi da Muhammadu Buhari.

Idan ba a manta ba Atiku ya yi fama da gwagwarmaya da gwamnatin Buhari inda aka yi ta kai ruwa rana tsakanin sa da hukumar kula da tashoshin ruwan Najeriya NPA, bayan ta dakatar da wasu ayyuka da ke karkashin kulan Kamfanin sa na INTEL.

Daga karshe dai a sami daidaituwa a tsakanin kamfanin da hukumar NPA.

Share.

game da Author