An tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Imo

0

An tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Imo, Eze Madumere, kamar yadda gidan talbijin mai zaman kan sa na Channels ya ruwaito ba da jimawa ba.

An ruwaito cewa ‘yan majalisar dokokin jihar 19 daga cikin 37 ne suka tsige mataimakin na gwamnan Imo, Rochas Okoroha.

Dama tun da farko, majalisar ta karbi rahoton da kwamitin bincike ya mika mata, wanda babban mai shari’a na jihar ya kafa.

An kafa kwamitin ne domin ya binciki rashin da’a da kuma wata harkalla da aka zarge shi da aikatawa. Madumere ya dade ya na samun rashin jituwa tsakanin sa da Gwamna Rochas Okorocha, a kan abin da ya shafi wanda zai gaji gwamnan a zaben 2019.

Yayin da Madumere ke neman ya gaji Okorocha, shi kuwa Okorocha wani surikin sa ne ya amince zai tsaya takara, tunda wa’adin Okorocha zai kare ne a watan Mayu, 2019.

Yayin da bangaren APC ke goyon bayan Madumere da wani Sanata Osita Izunaso, kuma su ne uwar jam’iyya ta amince wa, sai kotu ta soke zaben na su.

An kasa samun Madumere domin jin karin bayani a daidai lokacin rubuta wannan labari.

Share.

game da Author