Ramalan Yero ya mika takardar tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a PDP

0

A yau Litini ne tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero ya mika takardar tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a inuwar jam’iyyar PDP.

Yero da dandazon magoya bayan sa sun garzaya ofishin jam’iyyar PDP dake garin Kaduna domin mika takardar tayawa takara a jam’iyyar.

Bayan ya mika takardar ya kuma godewa magoya bayan sa da wasu da dama da suka bashi shawarar tsayawa takarar gwamnan jihar.

Ya ce an sami matsalolin gaske tun bayan saukar su daga gwamnati, da ya sa yanzu ake ta fama da rashin zaman lafiya da ayyukan ‘yan ta’adda.

” Duk hakan a faru ne saboda gazawar masu mulki a jihar.”

” Kare rayukan mutane da dukiyoyin su na daya daga cikin ayyukan da gwamnati ta kamata ta maida hankali a kai amma wannan gwamnati ba su bane a gabanta.

” Jihar Kaduna na Bukatar shugaba mai hangen nesa da ke ta muradin talaka a zuciyar sa, wanda zai inganta rayukan su da ciyar da jihar gaba.”

Bayan Ramalan Yero akwai sauran yan takara kamar su Isah Ashiru, Sani Sidi, Mohammed Bello da ke neman tsayawa takarar gwamnan a jihar Kaduna.

Share.

game da Author