Matuka keke NAPEP sun toshe manyan titunan Maiduguri

0

Wasu ‘yan takifen matuka keke NAPEP a Maiduguri jihar Barno sun gudanar da zanga zanga inda suka hana motoci wucewa a wasu manyan tituna da hanyoyin Maiduguri.

Matuka keken sun koka kan yadda jami’an ‘yan sanda suke karbar cin hanci a hannun su na babu gaira babu dalili.

Bayanai sun nuna cewa a dalilin haka masu zanga-zangar sun toshe titunan jihar inda babu motar dake shiga ko fita daga garin Maduguri.

Da abin yaki ci yaki cinyewa sai da sojoji fatattaki masu zanga-zangar.

Wani cikin direbobin keke NAPEP mai suna Bala Isa ya bayyana cewa kungiyar su ‘All Commercial Motorcycle Riders Association of Nigeria (ACOMORAN)’ ba za su tashi daga wannan wuri ba ko da sojojin suka fatattake su.

Har yanzu dai rundunar ‘yan sanda da shugaban kungiyar ACOMORAN ba su ce komai ba game da wannan al’amari.

Share.

game da Author