A ranar Lahadi ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya bayyana cewa rundunar ta kama wani likita mai suna Olawale Raji da wata ma’aikaciyar jinya mai suna Fumilayo Olusegun kan kisan wata mata mai ciki da suka yi.
Oyeyemi ya ce rundunar ta daure ma’aikatan kiwon lafiyar ne ranar 26 ga watan Yuli bayan kanwar mamaciyar ta shigar da kara a ofishin su.
” Wata mazauniyar unguwar ireakari St Atan ota kanwar wata Aminat Iyanda Atisola mai suna Bose Kazeem ta shigar da kara a ofishin mu cewa wadannan ma’aikatan kiwon lafiya sun kashe yayan ta garin cire mata cikin wata biyu da take dauke da shi.
Ta ce Aminat ta fara samun matsaloli bayan cire cikin da wadannan ma’aikatan kiwon lafiya suke yi a cikin gidan Aminat wanda kafin su kai ta asibitin Abeokuta ta rasu a hanya”.
” Za mu kai su kotu da zaran mun kammala gudanar da bincike a kai.”
A karshe kwamishinan ‘yan sanda Ahmed Iliyasu ya yi kira ga mutane da sudai na zuwa wajen baragurbin likitoci idan basu da lafiya.
Ya ce zubar da ciki a kasar nan karya doka ce.