Jam’iyyar APC ta maida wa sanata da ke wakiltar Kaduna ta Arewa Suleiman Hunkuyi martani cewa ruwa ne ya kare wa dan kada ya sa ya ke ta amayo zantukan karerayi game da makomar siyasar sa ganin yanzu komai ya kwace masa a siyasar Kaduna.
Idan ba a manta ba Hunkuyi ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar APC kuma babu abin da zai sa shi ya dawo jam’iyyar kuma.
Hunkuyi ya ziyarci ofishin jam’iyyar PDP a Kaduna inda a wannan ziyara ya bayyana wa shugaban jam’iyyar Hassan Hyet cewa ya ziyarci ofishin jam’iyyar ne domin ya yi musu bisharar dawowar sa PDP da hada hannu da sauran ‘yan jam’iyyar domin ganin yadda zasu kada gwamna Nasir El-Rufai a 2019.
A takarda da mataimakin sakataren jam’iyyar APC na Kaduna Salisu Wusono ya saka wa hannu, jam’iyyar tace ruwa ne ya kare wa dan Kada.
” Idan ba a manta ba a 2003 Hunkuyi ya yi barazanar kada gwamnan jihar a wancan lokaci Ahmed Makarfi amma ya fadi zabe. Ina so in gaya muku cewa Hunkuyi bai taba cin zabe a jihar Kaduna ba sai da ya bi bayan gwamna El-Rufai a 2015.”
Hunkuyi dai sun sami sabani ne da gwamnan jihar Kaduna El-Rufai, bayan shiri da suka yi na tsawon lokaci tun bayan darewar wannan gwamnati.
Sai dai kuma abin da kamar yuwa domin yanzu ba sa ko ga maciji a tsakanin su. A sanadiyyar haka yasa gwamnatin jihar ta rusa wani gidan sa a dalilin rashin biyan kudin kasa.
APC a jihar Kaduna ta ce barazanar Hunkuyi ba zai dada ta da kasa ba ko kadan domin nagaba yayi gaba.
Sai dai kuma wani makusancin Hunkuyi ya bayyana mana cewa, gwamnatin Kaduna da APC na bare-bare ne kawai amma kowa ya jira yaga yadda za su dora hannu a ka suna kukan rashin hunkuyi.