Atiku ya yi tir da rikita-rikitar siyasar Benuwai

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi tir da halin da siyasar jihar Benuwai ke ciki, inda ‘yan majalisar dokokin jihar takwas kacal a cikin 30 suka tada kurar yakin shirin tsige gwamnan jihar Samuel Ortom.

Jami’an ‘yan sanda ne suka ba su kariya, inda suka shiga cikin majalisa, amma sai aka hana mafiyawan mambobin da suka koma PDP shiga cikin majalisar.

Wadannan mambobi ‘yan APC, sun shiga inda suka yi zaman aika wa gwamna sammacin sanar da shi shirye-shiryen tsige shi.

Da ya ke magana kan haka a yau Litinin, Atiku ya nuna cewa a gaskiya ya na jin kunyar abin da ke faruwa a jihar Benuwai.

Daga nan sai ya yi Allah-wadai da karfa-karfar da ake neman yi a tsige gwamna Ortom, ba tare da bin abin da kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadar ba.

Ya ci gaba da cewa duk wani yunkuri ko kulle-kullen da za a kitsa domin tsige gwamna, ba tare da bin tsarin da doka ta shimfida ba, ko kamar kururuwar kiran barkewar tashe-tashen hankula ne a jihar.

Daga nan sai ya nuna matukar bacin rai ganin yadda jihar da ke cikin fama da matsalar tsaro, maimakon a kawo karshen matsalar, sai kuma a sake yi wa al’ummar ta bi-ta-da-kullin kokarin tsige gwamna, domin a kara jefa jihar cikin wani sabon tashin hankali.

Atiku ya yi kira ga jami’an ‘yan sanda da su daina rufe ido su na nuna bangaranci wajen yi wa masu mulki abin da suke so, sabanin abinda doka ta umarci ‘yan sandan su rika kiyayewa.

Ya ce abin da aka sani ga ‘yan sanda shi ne bin umarnin abin da doka ta ce su yi, ba bin umarnin masu mulki ba.

Share.

game da Author