Ina gab da in koma PDP – Abdulfatah Ahmed

0

Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed ya bayyana cewa yana gab da ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Ahmed ya fadi haka ne a taron musayan ra’ayi da mutanen jihar da ya ke amsa tambayoyi daga wadanda suka halarci taron.

Ahmed yace babban abin da ke tada mai hankali shine gazawar da jam’iyyar APC tayi na cika wa mutane alkawurran da ta dauka.

Ya ce irin wadannan abubuwa ne ya sa yake sake zurfin tunani game da komai kuma wadannan dalilai na daga cikin abubuwan da ya sa nake ganin zan iya ficewa daga jam’iyyar.

Kungiyoyin da suka halarci wannan taro sun amince da wannan shawara da gwamna Ahmed ke so ya dauka.

Sun tabbatar masa cewa za su bishi sau da kafa sannan suna tare da shi 100 bisa 100 kan duk shawarar da yanke.

” Muma mutanen jihar jam’iyyar APC ta ishe mu, musamman ganin yadda suka sa shugaban mu Bukola Saraki a gaba, sannan kai ma ba su kyale ka ba. Sannan gashi babu wani abin azo a agni da gwamnatin ta yi wa mutane. Da zarar ka shirya, a shirye muke duk mu koma PDP.”

Share.

game da Author