Sanata Abdullahi Danbaba daga jihar Sokoto da kuma Sanata Isa Misau daga Bauchi, sun bayyana Sanata Abdullahi Adamu a matsayin gogarman kunna wutar rikici da rarrabuwar hadin kai a Majalisar Dattawa.
Cikin wata takarda da su biyun suka saka wa hannu, sun yi ikirarin cewa Sanata Adamu ya kasa zaune, ya kasa tsaye ne a Majalisa tun farkon kafa majalisa a 2015.
Sun ce dalili, saboda ya nemi shugabancin kwamiti an hana shi. Sai ya koma ya zama dan kuikuyon da fadar shugaban kasa ke raino, shi kuma ya na yi wa fadar bambadanci, saboda guntun kashin da ya ke bayan sa.
Danbaba da Misau sun ce a yanzu haka akwai guntuwar igiyar EFCC a wuyan Sanata Adamu inda ya ke da zargin harkalla shi da daya daga cikin ‘ya’yan sa.
Wannan dalilin ne ya sa Adamu ke ta shisshige wa Buhari, saboda tsoron kamun EFCC.
Sun kuma nuna rashin jin dadi ganin yadda dattijo kamar zai kantara wa Najeriya da Buhari karya wai Saraki ya saka sunayen sanatoci ba tare da ya shawarce su ba.
” Wai sanatocin daga jihar Kwara ne kawai suka canza sheka ba duka wadanda Sarakin a ambato a majalisa ba ne. Mu dai bamu san haka ba domin bamu san inda shi ya samu tasa bayanan ba.
” To mu na so ya san cewa da sanin mu duk aka saka sunayen mu kuma nan gaba ba da dadewa ba wasu ma za su biyo sawun mu.”